top of page

Babbar hanyar da za ka bi ka kare shafin Facebook daga masu kutse


Daga Dr. Tijjani Ɗaha





Tabbas, alƙinta muhimman bayanan ka na sirri a ƙafar Internet, ba ƙaramin aiki bane. A manhajar da masu kutse wa jama'a ke ta shige da ficen kan yadda za su sace bayanan jama'a. Yanzu yana da matuƙar wuya, mutum ya iya ware wata kafa ko manhaja ta ƙafar sada zumunta da zai samu cikakken tsaro na shafinsa. Amma mutum zai iya tsira daga sharrin su, idan ya yi amfani da lambobin sirri (Password) masu tsauri, wadanda za su yi wuyar ganewa. Sai sauya lambobin sirri (Password), akai-akai da kuma dai na haɗa wayarka da wata wayar don amfani da datar waccan wayar ta hanyar amfani da Wi-fi hotspots), musamman wanda Wi-fi hotspots ɗin a buɗe yake babu cikekken lambar sirri na tsaro, sai kuma mutum ya dai na shiga duk wani website ko links da wani zai turo masa wanda bai san asalin sa ba.



Yayin da matsalar rashin tsaron bayanan Jama'a a internet ke ƙara haɓaka saboda ayyukan masu kutse ta Internet a wannan lokaci, jama'a na ta kokawa kan yadda ake yi yawan yi musu satar bayanansu na sirri. Shi ya sanya, jama'a da dama yanzu su ka fara ɗaukar waɗannan muhimman matakai da na lissafo su tun da farko.



Sai dai duk da haka, akwai wasu mutanen da har yanzu ba su ɗauki waɗannan matakai ba, shi ya sa suke yawan faɗawa tarkon masu kutsen internet (Hackers). A muƙalar da zan gabatar yau, zan yi bayani ne kan muhimman abubuwan da mutum zai yi domin kare shafinsa (facebook Account) ɗin sa na facebook daga sharrin masu kutsen internet (Hackers), wanda ya shafi tsarin nan da ake wa lakabi da hanyoyi biyu na tabbatar da tsaro (two factor authentication).



Two factor authentication, wato hanyoyi biyu na tabbatar da tsaron shafi ko account na facebook. Wani tsari ne na ɗaukar matakan ba da kariya na tsaro ga shafi (facebook account) , wanda ba wai kawai lambobin sirri (Password) mutum ya ke buƙata ba domin tabbatar da cewa wannan shafi (facebook account) ɗin nasa ne, a,a, akwai wani gwaji na daban da za a yiwa mutum kafin akai ga tantance sahihancin ko shine ya mallaki shafin (Facebook account ɗin), ko akasin haka. Wannan yana nufi lokacin da mutum yayi yunƙurin shiga shafinsa na facebook (facebook Account) ɗin sa, akwai wasu ƙarin gwaji da za ayi masa kafin a amince shine wanda ya mallaki shafin Facebook ɗin. Yadda abin ya ke kuwa shine; website na Facebook zai turo masa da saƙo ta lambar wayarsa ɗauke da wasu lambobi, ko ta email ɗin sa, wanda shine zai bashi damar iya shiga shafinsa (facebook account ɗin sa). Wato wannan dai ya nuna cewa, ko da masu kutsen internet sun samu lambobin sirri ( password ɗin sa) da sunan shafin sa (username ɗin sa), ba za su iya ƙwace masa shafi (account ba).



Yadda ake shirya wannan hanyoyi biyu na bai wa shafi (facebook account) kariya kuwa (two factor authentication), yana da matuƙar sauƙi sosai. Mutum zai yi shine ta hanyar shiga ɓangaren tsaro (security), sai ya danna setting. Za kuma iya kallon faifan bidiyon yadda ake yin two factor authentication ɗin anan.



Bugu da ƙari, ya kamata mutane su lura da wannan matsala ita ma, saboda masu kutse suna da hanyoyi da yawa da suke bi domin aiwatar da ta'adin da su keyi, wanda idan kana yawan aikata wannan abin da zan faɗa yanzu to masu kutse za su iya ƙwace iko da duk shafukan ka na ƙafafen sada zumunta ko na internet. Misali, idan kai mutum ne mai amfani da lambobin sirri (password) iri ɗaya a dukkanin shafukan ka na sada zumunta, to masu kutsen Internet in suka ƙwace shafinka ɗaya na facebook, za su iya ƙwace sauran tare da sace bayanan ka baƙi ɗaya.



Domin tsira daga wannan matsalar, ka tabbata baka amfani da lambobin sirri (Password) iri ɗaya a dukkanin shafukan ka (account ɗin ka) na soshiyal midiya. Sannan ka guji amfani da haruffa masu sauƙin ganewa, Haka kuma ya kamata kasan cewa, wannan tsari na bai wa shafukan facebook (facebook account), tsaro na musamman ta hanyar two factor authentication, wajibi ne ga duk mai amfani da soshiyal midiya musamman Facebook, ba wai sai kaga dama za ka yi ba.



In takaice muku, yana da matuƙar muhimmanci kusan cewa, yayin da wannan tsari na bai wa shafin Facebook (facebook account) tsaro ta hanyar amfani da two factor authentication, ke da matuƙar tasiri wajen bai wa shafin ka na facebook kariya, a lokaci guda, zai iya zama babbar barazana gare ka, idan har baka san yadda za ka yi amfani da shi ba. Alal misali, masu kutse za su iya amfani da hanyoyin yaudara wajen samun bayanai a wajen mutum wanda za su iya amfani da shi wajen yin damfara, musamman wajen yaudarar mutum da ya turo musu da lambar OTP da facebook za su turo ma mutum da shi idan suka bukaci shiga shafin sa. Saboda haka yana da matuƙar muhimmanci kowa ya ɓoye lambar OTP ɗin sa da aka turo masa ta hanyar saƙon waya, ku guji bai wa wani lambobin OTP ɗin ku. Daga ƙarshe, idan har OTP ɗin ka za a turo maka shi ta hanyar saƙon waya ne to ka yi duk mai yiwuwa wajen kare layinka, ko da wasa kar ka bari layin wayarka ya shiga hannun wani, saboda idan ka rasa layin wayarka to dai-dai yake da ka yi asarar shafinka na facebook (Facebook account), sai dai in kana da wani tsari na tsaron na amfani da email.

 
 
 

Comments


Powered by YourKnowledgeCompanion             

 ©2022 dahatijjani.  All rights reserved

bottom of page